15 Nuwamba 2021 - 16:59
​Siriya da Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Tattauna Kan Hanyoyin Bunkasa Tattalin Arziki A Tsakaninsu

Ministan tattalin arziki da cinikayya na kasar Siriya Mohammad Samer al-khalil ya gana da takwaransa na hadadiyar daular larabawa Thani bin Ahmad Alzeyudi domin duba irin sabbin tsare-tsaren da za’a bullo da su domin inganta huldar tattalin arziki da kuma yin musaya a wasu muhimman harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Dukkan kasahen biyu sun jaddada game da muhimmancin habaka harkar sufiri tsakaninsu, wanda zai bada yanayi mai kyau na musayar kayayyakin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu, da kuma kawar da shingen da ke hana musayar kayyaki wadada kasashen samarwa tsakaninsu.

Masana tattalin arziki na bayyana wannan mataki a matsayin wani ci gaba mai muhimmanci, musamman idan aka yi la’akari da matsalolin tattalin arzikin da kasar Siriya ke ciki sakamakon yakin da ta aka kwashe shekaru 10 ana yi a kasar, wanda ‘yan ta’adda dake samun goyon bayan wasu kasashen suka dora mata.

342/